Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa yayin tarukan siyasa a sassan ƙasar, tare da gargaɗin ’yan siyasa da magoya bayansu su guji tayar da tarzoma.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2026, Tinubu ya buƙaci ‘yan siyasa su mayar da hankali kan manufofin inganta rayuwar al’umma maimakon amfani da tashin hankali.
Shugaban ya kuma umarci jami’an tsaro su ɗauki matakan da doka ta tanada kan duk wanda aka samu da hannu a rikicin siyasa, yana mai jaddada aniyarsa ta ganin an gudanar da zaɓen 2027 cikin lumana, ’yanci da adalci.
