Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta rahotannin da ke cewa, ya yi alƙawarin bai wa ‘yan majalisar dattawa da suka fadi zaɓen fidda-gwani na jam’iyya tikitin takarar sanata kai tsaye na komawa majalisa.
A cikin wata sanarwa daga ofishinsa, ya ce abin da ya yi shi ne nuna tausayawa ga ‘yan majalisar da abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa shugabancin jam’iyyar APC na duba rikice-rikicen da suka taso daga zaɓukan fidda-gwani.
Mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Eseme Eyiboh, ya ce Godswill Akpabio bai yi wani alƙawari na ba da tikiti ba, kuma rahotannin da ke yawo ba su da tushe.
Ya kuma jaddada cewa Majalisar Dattawa za ta ci gaba da yin aiki cikin bin doka da tsarin jam’iyya, ba tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar APC ba.
