Hukumar zabe INEC ta tsawaita wa’adin rajistar masu kaɗa ƙuri’a da makonni biyu, inda yanzu za a kammala rijistar a ranar 26 ga Yulin da muke ciki.
A cikin wata sanarwa, Kwamishinan INEC mai kula da Yaɗa Labarai Mohammed Haruna, ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa duk ‘yan Najeriya da suka cancanta damar yin rajista.
INEC ta sanar da ƙaddamar da tsarin rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta yanar gizo ga sabbin masu rajista, wanda zai fara aiki daga 8 ga Yulin da muke ciki.
Hukumar ta buƙaci duk waɗanda ba su yi rajista ba su yi amfani da wannan ƙarin lokaci, tare da jaddada aniyarta na tabbatar da sahihancin rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta hanyar amfani da fasahar zamani.
