U.S. President Donald Trump looks on as he meets with the White House Task Force on the FIFA World Cup 2026 in the Oval Office at the White House in Washington, D.C., U.S., November 17, 2025. REUTERS/Evelyn Hockstein
Shugaban Amurka Donald Trump ya gargaɗi Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu cewa nan gaba kaɗan zai iya barinsa ya je ya ƙarata da Iran matuƙar ya ci gaba da rura wutar yaƙi.
Kamfanin dillancin labaran Isra’ila ya ba da rahoto a yau Litinin cewa Netanyahu bai faɗawa Trump game da shawararsa ta baya-bayan nan ta kaiwa Iran hari a ranar Lahadi ba, har sai da lokacin ya ƙure a matakin tsarawa.
Trump ya nemi Netanyahu a ranar Lahadi ya guji kaiwa Iran harin ramuwar gayya kan harin da aka kaiwa Isra’ila bayan ta ƙaddamar da hari a Beirut, babban birnin Lebanon.
Hirar ta ƙare ne ba tare da cimma yarjejeniya ba kuma Netanyahu bai sanar da Trump ba game da shawararsa ta ƙarshe a kan batun, kamar yadda tashar Channel 12 ta ruwaito.
Daga bisani, Netanyahu ya sanar da Sakataren Wajen Amurka Marco Rubio cewa ya yanke shawarar kaiwa iran hari.
Trump ya ja kunnen Netanyahu a kan ya guji rura wuta don kada yaƙi ya sake barkewa da Iran.
