Saurari premier Radio
30.6 C
Kano
Monday, September 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar zaɓen kasar nan INEC ta sanar da ɗage karɓar sakamakon zaɓen...

Hukumar zaɓen kasar nan INEC ta sanar da ɗage karɓar sakamakon zaɓen gwamnan Bayelsa zuwa ƙarfe 12:00 na yau Litinin.

Date:

Hukumar zaɓen kasar nan INEC ta sanar da ɗage karɓar sakamakon zaɓen gwamnan Bayelsa zuwa ƙarfe 12:00 na yau Litinin.

Hakan ya faru sakamakon cigaba da karbar sakamakon zaben a matakan rumfuna da mazaɓu a ƙananan hukumomin Brass da Ijaw ta Kudu da suka rage.

Shugaban sashen hulda da jama’a da ilimartar da masu kaɗa ƙuri’a na hukumar zaɓen Jihar, Wilfred Ifogah ya ce an sake gudanar da wasu zaɓukan a wasu mazaɓu da rumfunan zaɓe a ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu.

Ya kuma ƙara da cewa sakamakon yanayin da wuraren ke ciki, hukumar ta ɗauki matakin ɗage karɓar sakamakon zuwa yau Litinin, domin ba su damar kammala tattara sakamakon a matakan ƙananan hukumomi.

A jiya dai cikin kananan hukumomi takwas dake jihar an sanar da sakamakon kananan hukumomi shida wanda PDP tayi nasara a guda biyar yayin da APC tayi nasara a karamar hukuma daya.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...