Jami’ar Bayero ta sanar da dakatar da rubuta jarrabawar dalibanta sakamakon tsunduma yajin aikin TUC da NLC
Jami’ar Bayero ta dauki matakin ne a wata sanarwa da ta fitar a daren jiya mai dauke da sa hannun Rijistaran makarantar Aminu Umar Abdullahi.
Jami’ar ta bukaci dukkanin dalibai su jira har zuwa lokacin da zasu samu wata sanarwa a nan gaba.
A ranar Talata 14 ga Nuwambar da muke ciki ne kungiyoyin Kwadago na kasa NLC da TUC suka tsunduma yajin aiki
