
Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar sallah.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren Ma’aikatar, Magdalene Ajani ya fitar a ranar Laraba.
Ministan ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan.
Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya da yafiya da haɗin kai wajen gina al’umma.
Sannan Minista Tunji-Ojo ya buƙaci al’umma da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaban ƙasa.
Ya yi fatan cewa bukukuwan sallah za su ƙara haɗin kai tsakanin mutane duk da bambancin addini da ƙabilanci da ake da su.
Haka kuma, ya yi kira ga jama’a da su yi bukukuwan ta hanyar tunawa da mabuƙata ta yadda za a taimake su.