Gwamnatin Kano ta bayyana shirin ta na mayar da ƙarƙashin gadar Kofar Nasarawa zuwa wurin shakatawa mai kyau irin na zamani, tare da dasa bishiyoyi domin ƙawata birnin Kano da inganta muhalli.
Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na kano, Hamza Safiyanu Kachako, ne ya bayyana hakan yayin rangadin duba wuraren tara shara a jihar, bisa rakiyar shugaban Hukumar kwashe shara ta REMASAB, Dr. Muhammad S. Khalil.
Kwamishinan ya ce gwamnatin Gwamna Abba ta himmatu wajen bunƙasa wuraren shakatawa da ƙawata Kano, yana mai cewa shirin zai taimaka wajen inganta muhalli da samar da kyakkyawan yanayin shakatawa ga mazauna jihar.
A yayin rangadin, tawagar ta ziyarci gadar asibitin Murtala da kewaye, harabar gidan rediyon Kano, filin wasanni na Mahaha da ke Kofar Na’isa da kuma gadar Kofar Nasarawa.
Kachako ya bayyana gamsuwarsa da tsaftar da aka samu a mafi yawan wuraren, tare da yabawa ma’aikatan hukumar REMASAB kan ƙoƙarinsu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito kwamishinan na yin kira ga al’umma da su ba da haɗin kai wajen tsaftace muhalli, ta hanyar zubar da shara a wuraren da aka tanada, yana mai jaddada cewa tsaftar muhalli nauyi ne da ya rataya a kan kowa, ba gwamnati da hukumomin tsafta kaɗai ba.
