Kwamishinan Sufuri ne ya bayyana hakan a wata ziyarar gani da ido tashar
Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano Alhaji Ibrahim Ali Namadi Dala ne ya bayyana wannan kudiri na gwamnatin jihar a ziyarar gani da ido da ya kai tashar mai ciki da mutane da kuma cinkoso.
A yayin ziyarar Kwamishinan ya nuna takaicinsa na irin wasu abubuwan da ya gani ke da alaka da lalacewar tarbiyya da rashin tsari a wasu sassa na tashar.
Namadi ya kuma ce, duk Jihar Kano babu tasha mai girmanta, ya kuma bayyana cewa, za’a fara aikin nan ba da dadewa ba.
“Domin na san gwaman a shirye yake ya ba da dama mna gabatar masa da rahotannin da suka gani.
“Gwamnatin za ta mayar da tashar ta zamani wacce jihar kano da sauran al’umma za su yi alfahari da ita.
“Gwamnati za ta tabbatar da cewa tashar ta zama mai tsafta da tsari, tare da samar da dakunan kwanan matafiya da wuraren hutu da kuma sauran abubuwan da suka dace domin jin dadin masu amfani da tashar”. Inji shi.
A jawabinsa a yayin ziyarar, shugaban Karamar Hukumar Tarauni Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure ya ce, babu shakka sun yi farin ciki da gwamna ya zabi tashar ta Unguwa Uku don yin wannan aikin.
“Gwamna yana da kokarin mai da hankali kan abin da zai kawo wa Jama’ar kano ci gaba da samar da tsaro da kuma gyaran tarbiyya.
“Bugu da kari, zamanantar da tashar zai samar da aiki ga al’ummar Kano, don haka ina kira ga jama’a da kuma direbobi da ke aiki a tashar da ku ci gaba da bai wa gwamnatin goyon baya.” Inji shi