Gwamnatin Jihar Kano ta yi alƙawarin shiga tsakani domin ganin sabon tsarin DMS da Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ta fito da shi bai haifar da matsala ga masu sana’ar sayar da wayoyi a jihar ba.
Kwamishinan Kasuwanci, Zuba Jari da Masana’antu na jihar, Hon. Ibrahim Namadi Dala, ne ya bayar da wannan tabbacin lokacin da ya karɓi ƙorafe-ƙorafen ƙungiyoyin ’yan kasuwar wayoyi, waɗanda suka kai kukansu ma’aikatar domin neman ɗaukin gwamnatin jihar.
’Yan kasuwar sun miƙa ƙorafin ne bisa damuwarsu game da sabon tsarin DMS da NCC ta bullo da shi, tare da neman gwamnatin jihar ta duba lamarin domin kare muradun masu sana’ar.
Kwamishinan ya tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta shiga cikin lamarin domin ganin an aiwatar da tsarin ba tare da jefa masu sana’ar sayar da wayoyi cikin wata matsala ba.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin jihar na sauraron ƙorafe-ƙorafen masu sana’o’i tare da neman mafita da za ta yi la’akari da muradunsu.
