Gwamnatin Kano ta ce ta kama gurɓatattun kayayyakin abinci da abin sha da darajarsu ta haura naira miliyan 300 cikin ƙasa da watanni huɗu, yayin da wasu daga cikin ƴan kasuwar jihar ke ƙoƙarin sayar da su ga jama’a.
Shugaban Hukumar kare haƙƙin masu sayen kayayyaki ta jihar Dr Ibrahim Garba Muhammad ne ya bayyana hakan yayin da yake bajekolin kayan da hukumar ta kama a gaban manema labarai.
Dr Ibrahim ya ce kayayyakin da aka kama sun haɗa da waɗanda wa’adin amfaninsu ya ƙare da kuma waɗanda aka adana ba bisa ƙa’ida ba da wadanda jabu ne, lamarin da ka iya jefa rayuwar al’umma cikin haɗari idan aka bari aka sayar da su.
Dr Garba ya ce hukumar ta ƙara zage dantse wajen yin sintiri da bincike a kasuwanni da wuraren ajiyar kayan ‘yan kasuwa domin gano masu safarar gurɓatattun kayayyaki, tare da ɗaukar matakan doka a kansu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito shugaban hukumar na yin kira ga ƴan kasuwa da su guji sayar da kayan da ka iya cutar da lafiyar jama’a, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka samu da hannu a irin laifukan , tare da bukatar al’umma su riƙa duba inganci da wa’adin amfani da kowane kaya da suke saya.
