Gwamnatin Kano ta hannun Ma’aikatar albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta fara karɓar koken al’ummar jihar masu buƙatar a gina musu rijiyoyin burtsatse domin samar da agajin gaggawa ga yankunan da ke fuskantar ƙarancin ruwa.
Shirin na daga cikin rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da samarwa, waɗanda ake sa ran za su samar da lita miliyan 4 da dubu 140 na ruwa a kullum domin inganta samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar jihar.
Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr Dahiru Muhammad Hashim, ya ce an ƙaddamar da shirin ne domin samar da mafitar gaggawa ga al’ummomin da ke fama da matsalar samun ruwan sha, yayin da gwamnati ke ci gaba da aiwatar da gyare-gyare na dogon lokaci a cibiyoyin tace ruwa na Tamburawa da Challawa da kuma rumbun ajiyar ruwa na Goron Dutse.
Dr Hashim ya ce akwai buƙatar daukar matakan gaggawa ga yankunan dake fama da matsanancin ƙarancin ruwa ta hanyar samar da rijiyoyin burtsatse guda 166 da da gwamnati ta amince da su.
Dr Dahiru ya ƙara da cewa aikin gyaran manyan cibiyoyin samar da ruwa na tafiya yadda ya kamata, kuma ana sa ran kammala su cikin watanni takwas daga lokacin da aka fara aikin, lamarin da zai inganta samar da ruwa a birnin Kano da kewaye.
Kwamishinan ya buƙaci shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki da su cike fom din buƙatunsu ga sashin neman rijiyar burtsatsen ma’aikatar dake yanar gizo domin tantance yankunan da suka fi buƙata, inda masu neman tallafin zasu cike bayanai kamar suna, lambar waya, ƙaramar hukuma, gunduma da kuma adadin mutanen da za su amfana.
