Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bawa kowane ɗan jihar ƴancin gudanar da addininsa cikin walwala ba tare da tsangwama ba, domin ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya mabanbantan addinai.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin wakiliya ta musamman ta Majalisar Ɗinkin Duniya kan ‘Yancin Addini ko Akida, Farfesa Nazila Ghanea, wadda ta zo kano a wani ɓangare na binciken da ake gudanarwa a faɗin Najeriya kan batutuwan da suka shafi ‘yancin addini da akida.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan wanda Sakataren Gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya wakilta, ya yi maraba da tawagar tare da bayyana Kano a matsayin jihar da ta daɗe tana zama abin koyi wajen zaman lafiya da mutunta juna tsakanin mabiya addinai.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa na ci gaba da tallafawa manufofi da hukumomin da ke ƙarfafa zaman lafiya, tabbatar da adalci da kuma kare haƙƙoƙin kundin tsarin mulki na dukkan mazauna jihar ba tare da la’akari da addininsu ba, tare da magance duk wasu ƙalubalen da ka iya tasowa ta hanyar doka domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A nata jawabin, Farfesa Nazila Ghanea ta ce manufar ziyarar shi ne tantance yadda ake aiwatar da ‘yancin addini ko akida a Najeriya, ciki har da tanade-tanaden kundin tsarin mulki, matakan hukumomi, ƙalubalen da wasu bangarorin addinai ke fuskanta, tasirin al’adun gargajiya da kuma ƙoƙarin da ake yi wajen magance wariya da rikice-rikicen addini idan sun taso.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na yabawa gudunmawar da masu rike da sarautun gargajiya suke takawa wajen hada kan al’ummar da suke jagoranta duk da irin banbancin addini da akidun da suke da shi.
