Gwamnatin Kano ta bai wa kwamitin da ta kafa domin binciken zarge-zargen cin hanci da rashawa a kwalejin koyon aikin jinya ta jihar wa’adin kwanaki uku domin kammala bincike tare da miƙa mata rahotonsa.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, wanda ke jagorantar kwamitin ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman farko na kwamitin.
Bature ya ce kwamitin zai gudanar da bincike mai zurfi domin tantance sahihancin zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yiwa shugabar kwalejin da sauran manyan jami’an dake kula da ita, tare da gabatar da shawarwarin da suka dace ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwamishinan ya ce kwamitin zai gudanar da binciken sa cikin gaskiya, adalci da rashin nuna bambanci, domin gano hakikanin gaskiyar zarge-zargen kafin miƙa rahotonsa ga gwamnati cikin wa’adin kwanaki ukun da aka ba shi.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, sauran mambobin kwamitin sun haɗa da babban sakataren ma’aikatar lafiya ta Kano, Alhaji Abdulkadir Shehu, wasu jami’an gwamnati, wakilan hukumar karɓar Ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa, da kuma ƙungiyoyin ƙwararrun ma’aikatan jinya.
