Gwamnatin Kano ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Gidauniyar Dangote, domin miƙa mata Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Dangote da ke JIHAR na tsawon shekaru 20.
Da yake jawabi yayin sanya hannun, Sakataren Gwamnatin Kano Umar Farouk Ibrahim ya jinjinawa Gidauniyar ta Dangote bisa ci gaba da tallafawa shirye-shiryen bunƙasa ƙwarewar matasa da inganta rayuwar al’umma, inda ya ce haɗin gwiwar zai baiwa matasa damar koyon sana’o’i da dabarun fasaha domin dogaro da kansu.
Umar Farouk ya ce cibiyar za ta samar da damarmaki ga matasa wajen koyon sana’o’in hannu da dabarun kasuwanci, waɗanda za su taimaka musu wajen kafa sana’o’insu tare da bayar da gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Kano.
Ya ce miƙa cibiyar wani mataki ne na ƙara ƙarfafa ƙoƙarin gwamnatin Kano wajen rage rashin aikin yi da samar da hanyoyin dogaro da kai masu ɗorewa ga al’ummar Kano.
A nata ɓangaren, Gidauniyar Ɗangote wanda Manajan ta mai kula da shiyyar arewa maso yamma Sunusi Abdulkadir ya wakilta, ya jaddada aniyar gidauniyar na ci gaba da tallafawa shirye-shiryen ilimi, koyar da sana’o’i da ƙarfafa tattalin arziƙi, musamman tsakanin matasa.
