Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhinin sa bisa rasuwar fitaccen mawaƙin siyasa, Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka, wanda ya rasu yana da shekaru 47 a duniya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Sanarwar ta ce an shirya yiwa marigayin jana’iza da misalin ƙarfe biyar na yammacin yau Lahadi a ƙauyen Tsanni da ke ƙaramar hukumar Batagarawa a Jihar Katsina.
Gwamna Abba ya bayyana marigayin a matsayin ɗan asalin jihar Katsina mai kishin ƙasa wanda ya yi fice a Kano, inda waƙoƙinsa suka kasance hanyar inganta haɗin kai, inganta al’adu da wayar da kan al’umma.
Gwamnan ya ce Kosan Waka na daga cikin fitattun mawaƙan siyasa a Kano, kuma ya yi suna saboda hazakarsa da irin gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa harkokin siyasa da nishaɗantarwa cikin harshen Hausa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf ya roƙon Allah da ya gafartawa marigayin, ya yalwata kabarin sa tare da shigar da shi Aljannatul Firdaus.
