Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya taya al’ummar jihar murnar zagayowa bikin Takutaha, wanda ake gudanarwa duk shekara domin tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar,.
Gwamna Yusuf ya bayyana Takutaha a matsayin muhimmiyar al’adar addini da al’adu wadda ke hada kan al’ummar Kano wajen bayyana kaunar Annabi Muhammad (SAW) da tunawa da kyawawan dabi’u da koyarwarsa.
Gwamnan ya ce bikin na daga cikin dimbin al’adun addinin Musulunci na Kano, yana mai cewa al’ummar jihar sun shafe shekaru aru-aru suna kokarin karewa da ci gaba da gudanar da bukukuwan addini da al’adu da suka shafi Mauludi.
Ya kuma bukaci Musulmi da su yi amfani da lokacin wajen sabunta alkawarinsu na bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW), musamman kan zaman lafiya, tausayi, hakuri, adalci da zaman tare cikin lumana, tare da yin kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da rike hadin kai da zumunci domin samun ci gaba mai dorewa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na yabawa sarakunan gargajiya, malamai, shugabannin al’umma da masu shirya bikin bisa kokarinsu na kare al’adun addini da tarihi na Kano, inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa shirye-shiryen da ke inganta tarihi, al’adu da dabi’un addini.
