Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da cibiyar daƙilewa da kula da cututtuka ta jihar, a wani mataki na ƙarfafa tsarin kiwon lafiya da dakile yaɗuwar cututtuka.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da cibiyar, Gwamna Yusuf ya bayyana farin cikinsa da kammala aikin, wanda shi ne ya aza harsashinsa, yana mai cewa cibiyar wata babbar nasara ce a ƙoƙarin gwamnatin sa na gina ingantaccen tsarin kiwon lafiyar da zai iya fuskantar barazanar cututtuka cikin gaggawa.
Ya ce cibiyar za ta taimaka wajen sanya ido kan yaɗuwar cututtuka, gano su da wuri, dakile yaduwarsu da kuma inganta matakan gaggawa, tare da ƙara ƙarfin jihar wajen kare al’umma daga sabbin cututtuka da kuma waɗanda ke sake bayyana.
Tun da farko a jawabin sa, Kwamishinan lafiya na Kano, Dr Abubakar Labaran Yusuf, ya ce cibiyar za ta taka muhimmiyar rawa wajen hanawa, ganowa, sanya ido da kuma shawo kan cututtuka masu yaɗuwa kamar tarin fuka, kwalara, cutar kanjamau da sauran cututtuka.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Labaran na cewa an tanadi cibiyar da na’urori na zamani da ƙwararrun ma’aikata domin inganta gano barkewar cututtuka da wuri da kuma haɗa kai da sauran hukumomi da ƙungiyoyi masu zaman kan su wajen kare lafiyar al’umma.
