Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce jihar na da ɗimbin damarmakin da za ta iya amfani da su wajen zuba jari a harkokin ƙirƙire-ƙirƙire, sana’o’i da kasuwanci domin ƙara haɓaka tattalin arzikin jihar da ƙasa baki ɗaya.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne lokacin da ɗaliban babban Kwas na 48 na cibiyar nazarin manufofi da dabaru suka kammala rangadin nazari kan ayyukan gwamnatin Kano da suka gudanar na kwanaki 7 a jihar.
Gwamnna wanda mataimakinsa Murtala Sule ya wakilta, ya ce rangadin ya baiwa tawagar damar ganawa da hukumomin gwamnati, sarakunan gargajiya, ‘yan kasuwa da sauran al’umma, tare da ziyartar muhimman wuraren tarihi da kasuwanni.
Gwamnan ya bayyana fatan cewa, rangadin na su zai taimaka musu wajen fahimtar yanayin ci gaban Kano, ƙalubalen tattalin arzikinta da kuma irin damar kasuwanci da ƙwarewar da jihar ta shahara da ita.
Da yake jawabi, Shugaban tawagar, Birgediya Janar L.A. Jimoh, jinjinawa Gwamnati Kano kan ƙoƙarinta na bunƙasa harkokin ƙirƙire-ƙirƙire da kasuwanci, inda ya ce tarihin Kano a harkokin kasuwanci, masaƙu, sarrafa fata, noma, masana’antu, sana’o’in hannu da sauran harkokin ƙirƙire-ƙirƙire ya sanya jihar cikin kyakkyawan matsayi na cin gajiyar tattalin arzikin ƙirƙire-ƙirƙire.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Janar Jimoh na cewa akwai dimbin damammaki a fannonin sana’o’in gargajiya, fina-finai, kafafen yaɗa labarai, kiɗa, wallafe-wallafe, yawon buɗe ido da harkokin kasuwanci na zamani, a matsayin matakan da za su taimaka wajen baiwa dubban matasan jihar ƙwarewa, kayan aiki da tallafin fara sana’a.
