Gwamnan jihar Osun kuma ɗan takarar jam’iyyar Accord, Ademola Adeleke ya fara samun nasara a rumfar zaɓensa, bayan jam’iyyarsa ta Accord ta samu ƙuri’u 57, yayin da APC ta samu 43 a rumfar zaɓe mai lamba 026, Ward 5, Osogbo.
Gwamnan ya lashe akwatin zaɓe na farko da aka sanar da sakamakonsa a zaɓen gwamnan jihar da ake gudanarwa.
Jami’an hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, sun bayyana cewa jam’iyyar Accord ta samu nasara a akwatin zaɓe mai lamba 026, da ke Ward 5 a ƙaramar hukumar Osogbo.
Rahotanni sun ce yanzu haka sakamakon zaɓe daga wasu rumfunan zaɓe a faɗin jihar ya fara fitowa a hankali.
A yayin da ake ci gaba da zaɓen, an samu rahotannin zargin tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a, sayen ƙuri’u da kuma wasu matsalolin tsaro a wasu wurare.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa zaɓen na gudana cikin nasara a wasu sassan jihar.
