Kwalejin Nazarin Shari’a da addinin Musulunci wato LEGAL ta roƙi gwamnatin Kano da ta ƙara tallafa mata tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da ita, domin magance matsalolin da ke fuskantar makarantar da kuma inganta yanayin karatu ga ɗalibai.
Mukaddashin Shugaban kwalejin , Dr Ali Tamasi Mu’azu, ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci shugabannin kwalejin zuwa ziyarar aiki ga Kwamishinan yaɗa labarai na Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya.
Dr Mu’azu ya ce ziyarar na da nufin ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin kwalejin da gwamnatin Kano, musamman wajen kula da jin daɗin ɗalibai da ma’aikata, samar da kayayyakin more rayuwa da sauran abubuwan da kwalejin ke buƙata.
A nasa martanin, Kwamishina Ibrahim Abdullahi Waiya ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati wajen gano tare da magance matsalolin da ka iya kawo cikas ga ayyukan ilimi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta duba buƙatun kwalejin tare da ba su kulawar da ta dace.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito shugaban kwalejin Dr Tamasi na cewa kwalejin na taka muhimmiyar rawa wajen horar da ɗaliban da suke bayar da gudunmawa a harkokin shari’a da sauran fannonin da ke buƙatar ilimin dokoki.
