Gwamnatin Tarayya ta hannun ofishin jakadancinta da ke Johannesburg, ta yi Allah wadai da kisan wani ɗan ƙasarta, Ibeh Chika Simon, wanda ya mutu a yayin wani samamen da ‘yansandan Afirka ta Kudu suka kai a Bellville da ke Cape Town a ranar 23 ga Yuli.
Jakadancin ya ce mutuwar tasa ta faru ne a yanayi mai cike da tambayoyi, yayin da kuma wani ɗan Najeriya, Egwabor Patrick Chuks, ya samu munanan raunuka bayan an harbe shi a wannan samame.
A wata sanarwa, ofishin jakadancin ya ce ya yi matuƙar kaɗuwa da yadda lamarin ya faru, yana mai zargin jami’an tsaro da amfani da matakan da suka kai ga mutuwar marigayin.
Najeriya ta buƙaci hukumomin ƙasar su gudanar da bincike cikin gaggawa, adalci da gaskiya tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.
A nasa ɓangaren, Kwamitin Ministoci kan Harkokin Hijira na Afirka ta Kudu ya ce ana ci gaba da binciken abin da ya faru.
