Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya nuna matuƙar alhini da jimamin rasuwar mutanen da wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a karamar Hukumar Gezawa.
Lamarin ya faru ne a safiyar Lahadi a Kwanar Barde.
Sakon alhinin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu.
“Hatsarin abin tausayi ne kuma mai matukar muni, ga iyalan da lamarin ya shafa, da al’ummar Kano baki ɗaya”. In ji gwamnan.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya jikan mamatan, tare da roƙon Allah Ya bawa waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa.
Ya kuma bayar da umarnin Ma’aikatar Lafiya ta Kano da ta tabbatar ta ba wa waɗanda ke kwance a asibitoci cikakkiyar kulawar lafiya kyauta,
Sannan ya gargadi direbobin manyan motoci da su guji tukin ganganci domin kare faruwar irin hatsari a gaba.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya shafi wata tirela ne dake kan hanyarta na zuwa Gujungu, ana kuma zargin tukin ganganci ne ya haddasa hatsarin.
Lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutum talatin, yayin da wasu da dama suka jikkata.
