
Daruruwun motoci ne da direbobi da kuma fasinjoji suka maƙale tsawon sa’o’i kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sakamakon wani gagarimin cunkoson ababen hawa kan hanyar a yayin da ake shirin gudanar da bikin babbar sallah gobe.
Rahotani na cewa lamarin ya fi ƙamari a daidai yankin Bishini wasu kuma suka ce tun daga garin Jere ake ganin jerin motoci a kowanne hannu suna neman hanyar wucewa.

BBC ta rawaito cewa, dubban matafiya ne ke ta kokarin isa garuruwansu domin gudanar da bukukuwan Sallah tare da ‘yan uwa da abokan arziki amma ya gagara.
Hanyar Abuja zuwa Kaduna ɗaya ce cikin manyan hanyoyin da ke haɗa Babban Birnin Tarayya da jihohi da dama na arewacin Najeriya, ciki har da Kano da Neja.
Hotunan da matafiya ke wallafawa a shafukan sada zumunta na nuna dogayen layukan motocin daga Jere zuwa Katari – wurin da ya dade yana fuskantar irin wannan matsala a lokutan bukukuwa.
Zuwa yanzu hukumomi ba su komai ba game da musabbabin cunkoson ko matakan da ake ɗauka domin kawo ƙarshen matsalar.