Saurari premier Radio
24 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnan Kano Abba Kabir ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan mahaifiyar tsohon...

Gwamnan Kano Abba Kabir ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mahaifiyar tsohon shugaban kasa ‘Yar Adua a jihar Katsina.

Date:

Gwamnan Kano Abba Kabir ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mahaifiyar tsohon shugaban kasa ‘Yar Adua a jihar Katsina.

Aminu Abdullahi Ibrahim

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Yar’aduwa bisa rasuwar Mahaifiyar tsohon shugaban kasa Alhaji Umaru Musa Yar’aduwa Hajiya Dada Yar’aduwa.

Yayin ziyarar gwamna Abba Kabir Yusuf, yayi addu’ar Allah ya jaddada rahma ga Hajiya Dada da kuma mika ta’aziyya ga gwamnatin Katsina da al’ummar kasar nan baki daya.

Ya ce rasuwar Hajiya Dada rashi ne Daya shafi al’ummar kasar nan ba iya jihar Katsina ba.

Da yake jawabi daya daga cikin iyalanta Sanata Abdulaziz ‘Yar Adua, amadadin iyalai ya godewa gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa ta’aziyyar da yaje musu.

Abdulaziz ‘Yar Adua ya kuma yiwa gwamna Abba Kabir Yusuf addu’ar Allah yayi riko da hannayen sa wajen sauke nauyin dake kansa.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...