Matatar man fetur ta Dangote ta tsawaita wa’adin sayar da hannun jarinta ga al’umma na tsawon makonni biyu, inda sabon wa’adin zai kare a ranar 27 ga Oktoba, 2026.
Matatar ta dauki wannan mataki ne domin bayar da karin lokaci ga masu zuba jari da sauran al’umma da ke da niyar sayen hannun jarin.
A ranar ranar 14 ga Satumba ne matatar man Dangote ta buɗe damar sayen hannun jarin ga jama’a, da nufin tara kuɗaɗen da za su taimaka wajen faɗaɗa ayyukanta
