Hukumar EFCC ta ce, za ta fara kamen masu likin kudi a yayin shagalin biki da kuma kai kotu domin a hukunta su. Ya kuma ce kwanan za su fara zuwa even-even domin yin kame
Daraktan shiyyar hukumar a Kano Ibrahim Shazali, ne ya bayyana haka lokacin da kungiyar ba da agajin gaggawa ta Red Cross ta kai ziyara ofishin hukumar a ranar Litinin.
Daraktan ya bayyana likin kudin da ake yi a irin wadannan taruka da cewa almubazzaranci ne da rashin kishin kasa ba kuma za su lamunta ba.
“To, gaskiya doka yanzu ta ba mu damar bi duk wuraren da muka gani ana wurgar da kudi ana taka wa, ana yin abin da aka ga dama.
“Muna jan kunnen mutanen da suke zuwa bukuwa da su daina irin wannan almubazarancin watsa kudi da tattakasu da su daina.
“Domin kwanan nan za mu soma zuwa ‘event-event centers’ din nan, in mun kama mutum ya na lika kudi, za mu kamo shi mu kulle, kuma za mu kai shi kotu.” Inji shi.
Daraktan ya kuma ya bayyana takaicinsa na ganin yadda mutanen wasu kasashe suke alkinta takardar kudinsu da za ka gani an buga sama da shekarua 10 amma ka gan su fes a yanzu.
Amma takardun Naira daga an buga su kwanaki kadan sun lalace saboda yadda ake tattaka su a wurin biki da sauransu.
A kwanan baya ne hukumar a jihar Legas ta kama tare da gurfanar da wata ‘yar fim da kuma Bob Risky, wani mata-maza a bisa zargin cin zarafin kudin sakamakon yin liki a taron biki.
Kuma Kotu ta daure su da ta same su da laifin aikata hakan a lokuta daban – daban.