Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamared Isma’ila Ibrahim Dutse, Shugaban Ƙungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshenJihar Jigawa ya sanya wa hannu.
Kungiyar ta buƙaci gwamnatin jihar da ta tarayya da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen aiwatar da dokoki tare da ɗaukar dabarun haɗin gwiwa daga fannoni daban-daban domin dakile matsalar.
Kungiyar ta ce kusan kaso 80 cikin dari na matsalolin dake addabar Najeriya a halin yanzu, suna da alaka ta kai tsaye da yadda shan miyagun kwayoyi ya ta’azzara musamman tsakanin matasa maza da mata.
Sanarwar ta bukaci gwamnati a dukkan matakai da masu ruwa da tsaki da su dauki dukkan matakan da suka dace domin shawo kan matsalar.
