
Aminu Abdullahi Ibrahim
Mutane 10 sun rasu yayin da wasu suka jikkata sakamakon fashewar wani bam da ’yan taʼadda suka dasa a hanyar Bagega zuwa Anka da ke Jihar Zamfara.
lamarin ya faru ne a ranar Talata 9 ga Yunin 2026 inda bam ɗin ya tashi da motar fasinja a kan hanyar.
Wani mazaunin yankin Hassan Kumba Bagega ya ce, zuwa daren ranar Talatar sun yi janaʼizar mutane 10 daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun mutu ne a wurin da lamarin ya faru, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa.
Al’ummar yankin sun yi kira ga hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki su taimaka wajen inganta tsaro da kuma aikin hanyar Dareta zuwa Tungar Kudaku, Bagega, Tubuki, Kawaye da Sabon Birni domin saukaka zirga-zirga da ayyukan jami’an tsaro a yankin.
