Majalisar Ƙoli ta Shari’a a kasar nan ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dokoki ta Ƙasa da kada su gaggauta gyaran Kundin Tsarin Mulki domin kafa ‘yan sandan jihohi.
Ta ce ya kamata a fara sauraren shawarwari ga masu ruwa da tsaki kafin yanke hukunci.
A cikin wata sanarwa da Sakatare Janar na Majalisar, Nafiu Baba Ahmad, ya fitar, an bayyana cewa duk da matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta, bai kamata a ɗauki ‘yan sandan jihohi a matsayin mafita ta gaggawa ba.
Ya ce batun na da matuƙar tasiri wurin yin adalci, haɗin kan ƙasa da makomar kasar nan.
Majalisar ta ce matsalolin tsaron ƙasar sun samo asali ne daga cin hanci da rashawa, rashin isassun jami’ai, raunin tattara bayanan sirri, tsofaffin kayan aiki da rashin kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.
daga bisani, ta nuna rashin gamsuwa da yadda Majalisar Dokoki ta Ƙasa ke tafiyar da batun, tana mai cewa bai samu damar buɗe ƙofar tuntuɓa da haɗa ra’ayoyin jama’a ba.
