Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin masu riƙe da muƙaman siyasa na gwamnatin tarayya waɗanda suka fito daga Kano tare da sauran jagororin Jam’iyyar APC a Fadar Gwamnatin jihar da ke Abuja.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Taron wanda aka gudanar ƙarƙashin ƙungiyar Tinubu Renewed Hope Appointees reshen Kano, ya haɗa manyan jiga-jigan APC domin tattauna makomar jam’iyyar a jihar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Sanarwar ta ce Mahalarta taron sun amince da bayar da cikakken goyon bayansu ga Shugaba Tinubu, la’akari da ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa Kano da ƙasa baki ɗaya.
Sun kuma yi alƙawarin tattara kuri’u da goyon baya ga Shugaba Tinubu da Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, domin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 a Jihar Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa tsohon Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, Shugaban APC na Kano, Umar Haruna Doguwa, ministoci, masu baiwa shugaban ƙasa shawara, shugabannin hukumomin tarayya da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa daga Kano ne suka halarci taron.
