An shiga jimami a kauyen Tudun Kusa da ke karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna, bayan wasu yara uku sun mutu sakamakon fadawa cikin masai yayin kokarin ciro wayar hannu da ta fada ciki.
Yaran, wadanda aka bayyana sunayensu da Najjashi, Mohammed da Ashafa, masu shekaru tsakanin 12 zuwa 15, sun shiga masan daya bayan daya domin ciro wayar Android mallakin wani magidanci mai suna Murtala.
Da yake zantawa da wakilinmu Kabir Bello Tukur, kansilan yankin, Hashimu Muhammad, ya ce yaran ukun ba daga gida daya suke ba.
Ya bayyana cewa Murtala ya yi alkawarin bai wa duk wanda ya iya ciro masa wayar Naira 1,000, lamarin da ya sa Najjashi, wanda shi ne karami kuma mai kimanin shekaru 12, ya fara shiga masan.
A cewar kansilan, masan ta kasance tsohuwar rijiya ce a baya, amma bayan da ruwan cikinta ya ƙafe sai aka mayar da ita bayan gida.
Hashimu ya ce bayan Najjashi ya shiga masan aka daina jin duriyarsa, lamarin da ya sa Mohammed, mai shekaru 13, wanda ke wurin, shi ma ya shiga domin gano abin da ya faru da shi.
Ya kara da cewa daga bisani Ashafa, mai kimanin shekaru 15, shi ma ya dage sai ya shiga domin gano halin da abokansa suke ciki, duk da kokarin hana shi da aka yi.
A wani yunkuri na gano halin da ake ciki a cikin masan, wani dattijo ya ba da shawarar a zura kaza a ciki, amma ita ma kazar ta mutu kafin ta kai kasan masan.
Daga bisani, mazauna yankin sun yi amfani da kugiya wajen fito da gawarwakin yaran ukun, inda aka yi jana’izarsu bisa tsarin addinin Musulunci.
An rufe masan bayan faruwar lamarin.
Mazauna kauyen da suka zanta da Premier Radio sun bayyana cewa lamarin ya girgiza al’umma, inda suka ce ba su taba fuskantar irin wannan musiba ba.
Wani mazaunin kauyen ya ce, “Ba mu taba ganin musiba irin wannan ba. Hankalinmu ya tashi matuka, yara uku sun mutu lokaci guda.”
A halin yanzu, al’ummar Tudun Kusa sun fara zaman makokin kwanaki uku domin jimamin wannan babban rashi.
