Daga Hafsat Buhari
Alamu sun nuna cewar an bude filin jirgin saman Khartoum, sakamakon saukar wani jirgin fasinja a filin jirgin saman Khartoum a karon farkon a cikin shekaru uku da ɓarkewar yaƙin basasa a kasa.
Sanarwar da Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta ƙasar ta fitar ta ce, jirgin farko na kamfanin Sudan Airways ɗauke da fasinjojin da ya ɗauko daga birnin Port Sudan ya sauka lafiya a Khartum, abin da ke tabbatar da cewa an sake buɗe filin jirgin.
- Burhan: Ba Za a Samu Zaman Lafiya a Sudan Ba Sai An Kawar da RSF
- Mayaƙan RSF sun amince da shiga yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Sudan
Duk da cewa Hukumar ba ta bayyana adadin mutanen da ke cikin jirgin ba, amma bayanai sun tabbatar da cewa akwai manyan jami’an gwamnati ciki kuwa har da Firaministan Kamil Idris.
A cikin kwanakin da suka gabata, a sanar da cewa shugaban ƙasar da majalisarsa da suka tashi daga Khartum tare da kafa matsuguni na wucin gadi a Port Sudan gabashin ƙasar, sun ce za su dawo Khartum ba da jimawa ba saboda an samun zaman lafiya.
Majalisar Ɗinkin Ɗuniya ta ce, bayan da dakarun gwamnati suka yi nasarar fatatakar dakarun RSF daga fadar gwamnati, zuwa yanzu aƙalla fararen hula milyan ɗaya da dubu 400 ne suka dawo a gidanjensu a birnin.
