Majalisar Dokokin Jihar Kano ta musanta zargin cewa tana jinkirta duba ƙudirin dokar yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar mata.
A wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaranta, Kamaluddeen Sani Shawai, ya sanya wa hannu, majalisar ta mayar da martani ga kalaman Shugaban Kwamitin Yaƙi da Shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi na jihar, Barrister Muhyi Magaji Rimin Gado, kan kalaman da ya yi yayin wata hira da manema labarai.
Majalisar ta bayyana cewa ta karɓi ƙudirin tare da gudanar da karatun farko, sai dai gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2027 ya sa aka ɗage ci gaba da nazarinsa saboda muhimmancin kasafin ga ayyukan gwamnati.
Ta ce ba ta yi watsi da ƙudirin ba, tana mai cewa dukkan ƙudurorin da ake gabatar mata suna bin matakan da dokokin majalisa suka tanada.
Majalisar ta kuma tabbatar da goyon bayanta ga yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da shaye-shayensu, tare da buƙatar Rimin Gado ya guji yin zarge-zargen da ba a tantance ba, waɗanda a cewarta za su iya kawo cikas ga haɗin gwiwar hukumomi wajen magance matsalar.
