Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta cewa ya taɓa sauraron tattaunawar wayar Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ko kuma ya umurci wani ya yi hakan.
Yayin ba da shaida a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, El-Rufai ya ce bai taɓa mallakar na’urar sauraron wayar mutane ba, kuma ba shi da ƙwarewar yin hakan.
Ya bayyana cewa kalamansa a hirar da ya yi da Arise Television a watan Fabrairu kalaman siyasa ne na ƙarin gishiri, ba ikirarin cewa ya aikata sauraron waya ba.
Shari’ar ta samo asali ne daga zargin da ya yi cewa ya samu labarin umarnin kama shi ta hanyar sauraron wata tattaunawar Ribadu. Har yanzu kotu na sauraron shari’ar.
