Ƙungiyar ƴan gwan-gwan ta kasa (NASWDEN) ta sanar da shirin tsunduma yajin aiki na makonni biyu daga ranar 1 zuwa 15 ga Oktoba, 2026.
Ƙungiyar ta kuma umarci mambobinta da su dakatar da kai tsofaffin ƙarafa zuwa kamfanonin da ke narkar da su, wajen samar da kayayyakin amfani da sauran bukatun da ake yi da ƙarafu nan.
Shugaban kungiyar na ƙasa, Abdulfatah Ogunwale, ne ya bayar da umarnin yajin aikin, bisa zargin da ƙungiyar ta yi na samun matsaloli, rashin daidaito da koke-koken da suka shafi harkokin mambobinta.
A cikin wata sanarwa da kakakin Ƙungiyar, Stephen Azubukwe, ya sanyawa hannu, wadda Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Aminu Hassan Soja, ya fitar a Kano, NASWDEN ta ce yajin aikin na iya zama na dindindin idan ba’a cimma matsaya mai gamsarwa da kamfanonin narkar da ƙarafan da abin ya shafa ba.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa wasu kamfanoni kan rage farashin tsoffin ƙarafa ba tare da sanarwa ba, lamarin da take cewa yana jefa ’yan kasuwar da suka sayi kayayyaki tare da kashe kuɗin jigilar su cikin asara.
A cewar ƙungiyar, irin sauyin farashin na ba zato ba tsammani na iya jefa dillalai cikin asarar da ta kai tsakanin Naira miliyan 3 zuwa 6 kan lodin mota guda.
