
Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar Astute Civil Society for Cultural and Humanity Development ta nuna damuwa kan cire sunayen wasu ’yan takara daga hukumar zabe INEC.
Cikin wadanda kungiyar ta nuna damuwa kan cire sunayensu a zaben 2027, akwai dan takarar gwamnan Kano a jam’iyar NDC Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, da mataimakinsa Mustapha Rabiu Kwankwaso.
Kungiyar ta kuma ambaci ’yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihohin Gombe da Ogun, Isa Ali Pantami da Oladipupo Ladi Adebutu.

A wani taron manema labarai da ta gudanar a sakatariyar kungiyar ’yan jarida a nan Kano a ranar Asabar, kungiyar ta bukaci INEC ta sake duba korafe-korafen wadanda abin ya shafa cikin adalci da gaskiya, tare da bayyana takamaiman dalilan cire sunayen kowane dan takara.
Kungiyar, ta bakin mai magana da yawunta, Comrade Ibrahim Ali, ta ce tana da masaniya kan bayanin INEC na cewa cire sunayen na da alaka da rashin cika wasu sharuddan doka game da rajistar mambobin jam’iyyun siyasa, bayan wani hukuncin Kotun Koli.
Sai dai ta jaddada cewa idan wani dan takara ko jam’iyya na da hujjojin da ke nuna an cire sunansa bisa kuskure, ya kamata hukumar ta yi bincike mai zaman kansa tare da daukar matakin gyara idan doka ta ba da damar hakan.
Kungiyar ta ce kiran nata ba na goyon bayan wata jam’iyya ko dan takara ba ne, illa tabbatar da adalci da bin doka, da kuma karfafa amincewar jama’a ga tsarin zabe.
Ta kuma yi kira ga ’yan siyasa, magoya bayansu da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankula, su guji kalaman tunzura jama’a, su kuma bi hanyoyin doka wajen warware takaddamar domin tabbatar da zaman lafiya.
