Majalisar dokokin ƙasar Birtaniya ta jinjinawa ƙoƙarin gwamnatin Kano kan sauye-sauyen da take aiwatarwa domin bunƙasa ilimi ta hanyar zuba jari, gyaran manufofi dan inganta koyarwa, waɗanda suke ci gaba da samun karɓuwa a duniya.
Hakan na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda ya ce yabawa jihar ne a taron ƙasa da ƙasa kan bunƙasa karatu da rubutu da aka gudanar a Majalisar dattawan Birtaniya a birnin Landan.
A wajen taron, babban jami’in ƙungiyar Universal Learning Solutions, Gary Foxcroft, ya jinjinawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jagorancinsa wajen farfaɗo da ilimi a Kano, yayin da tsohon Ministan Makarantu na Birtaniya, Sir Nick Gibb, ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta nuna ƙuduri mai ƙarfi wajen sauya fasalin ilimi wanda kai tsaye zai taimaka wajen inganta ilimin yara.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mai bashi shawara kan gyaran ilimi, Haladu Mohammed, ya shaidawa taron cewa ilimi shi ne babban abinda gwamnatinsa tafi baiwa fifiko, la’akari da yadda gwamnatin sa ta ware kaso mafi tsoka na kasafin kuɗinta ga fannin.
Gwamna Abba ya ce Kano tana da kusan ɗalibai miliyan biyar yanzu haka, kuma ta samar da makarantu na zamani dubu 8 da makarantun Alƙur’ani fiye da dubu 14 waɗanda da ake haɗawa da tsarin ilimin zamani, duk da irin ƙalubalen yara sama da miliyan ɗaya da basa zuwa makaranta da jihar ke fama da shi.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa gwamnatinsa ta ɗauki malamai kusan dubu 20 cikin shekaru uku da suka gabata tare da ƙaddamar da sababbin tsare-tsaren horas da malamai da kuma shirin mayar da yaran da suka daina karatu zuwa makaranta.
