Gwamnatin Kano ta bukaci samun karin hadin gwiwa tsakaninta da kamfanoni masu zaman kansu, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin farar hula, domin inganta ci gaban karkara da al’ummar jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bukaci hakan, yayin taron ƙoli kan ci gaban Karkara da gina al’umma mai dorewa, wanda aka gudanar fadar gwamnatin Kano.
Gwamnan wanda mataimakinsa Murtala Sule Garo ya wakilta, ya ce ci gaban karkara na daga cikin muhimman manufofin gwamnatin sa wajen samar da ci gaban tattalin arziki, walwalar al’umma da kare muhalli.
Gwamnan ya ce ci gaban Kano ya dogara ne da ƙarfi da kuma ƙwazon al’ummomin karkara, musamman ganin yadda noma, kasuwanci da ƙananan sana’o’i ke ci gaba da tallafawa tattalin arzikin jihar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito mataimakin gwamnan na cewa kudurin gwamnati na bunkasa birni da karkara ba zai cika ba, sai da haɗin gwiwa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki domin magance ƙalubalen da ke addabar yankunan karkara.
