Ƙungiyar kula da lafiyar matasa da bayar da bayanai ta AHIP, ta buƙaci ƙarin haɗin gwiwa tsakanin sarakunan gargajiya, shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Kano, hukumomin gwamnati da ƙungiyoyin fararen hula, domin dakile yawaitar ƙaura zuwa ƙasashen ƙetare ba bisa ƙa’ida ba dake neman zama ruwan dare a Jihar Kano.
Ƙungiyar ta yi kiran ne yayin wani taron tattaunawa da shugabannin gargajiya da manyan jami’an ƙananan hukumomi 44 na Kano da limamai, inda aka tattauna hanyoyin da za’a bi wajen wayar da kan matasa da mata game da haɗarin da ke tattare da ƙauran ba bisa ƙa’ida ba.
Da take jawabi a wajen taron, Shugabar Ƙungiyar ta AHIP Hajiya Mairo Bello ta ce taron ya haɗa wakilai daga ƙananan hukumomin Dala, Gwale, Kano Municipal, Ungogo, Tarauni, Nassarawa, Kumbotso, Fagge da Bunkure, ciki har da sarakunan gargajiya, hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin fararen hula, kungiyoyin mata da matasa da wakilan al’umma.
Mairo Bello, ta ce manufar shirin ita ce wayar da kan matasa da mata kan illolin ƙaura ba bisa ƙa’ida ba, da suka haɗa da fataucin mutane, cin zarafi, tilasta aiki, matsalolin lafiya da rasa rayuka.
A nasu ɓangaren, mahalarta taron, mai unguwar ‘yar akwa Raihana Layout dake Gundumar Darmanawa a Ƙaramar Hukumar Tarauni, Kwamared Jamil Wada, ya tabbatar da aniyar shugabannin gargajiya da ƙananan hukumomi wajen ƙarfafa wayar da kan al’umma, musamman matasa da mata, kan illolin ƙaura ba bisa ƙa’ida ba.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Mairo Bello na cewa ƙungiyar ba za ta hana mutane fita ƙasashen waje ba, sai dai tana ƙarfafa musu gwiwa ne kan su bi hanyoyin da suka dace kuma doka ta amince da su.
