Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na da damar lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a Jihar Kano, ko da ba tare da goyon bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.
Kwamitin ya kuma zargi tsohon gwamnan Kano da ƙoƙarin haddasa rarrabuwar kai tsakanin ’yan adawa, domin hakan zai iya taimaka wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu samun wa’adi na biyu.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na kwamitin, Kola Ologbondiyan, ya fitar, ADC ta soki kiran Kwankwaso na cewa Atiku ya janye takararsa domin bai wa Peter Obi dama.
Kola ya ce maimakon Kwankwaso ya mayar da hankali kan ƙalubalantar gwamnatin Tinubu kan matsalolin tsadar rayuwa, yunwa, talauci da rashin tsaro, sai ya fi mayar da hankali wajen sukar Atiku.
Ya kuma yi nuni da sakamakon zaɓen da marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya samu a Kano a shekarun 2003 da 2007, yana mai cewa nasarar Atiku a jihar ba ta dogara da goyon bayan Kwankwaso kaɗai ba.
Kwamitin ya jaddada cewa Atiku na da damar samun nasara a Kano duk da ra’ayin Kwankwaso kan yadda ya kamata ’yan adawa su tsara takarar shugaban ƙasa ta 2027.
