Tsohon ɗan takarar kujerar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, ya fice daga jam’iyyar tare da komawa jam’iyyar APC mai mulki a jihar.
Hamma Saleh, wanda ya fafata da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, a takarar tikitin gwamnan PDP, ya sanar da matakin nasa ne cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Gombe.
A cikin sanarwar, ya kuma yi kira ga magoya bayansa a faɗin jihar da su bi sahunsa wajen komawa APC tare da mara wa ’yan takarar jam’iyyar baya a dukkan matakan zaɓe.
Ficewarsa daga PDP na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a Gombe gabanin zaɓen 2027.
Matakin na iya yin tasiri ga tsarin siyasar jihar, musamman ganin takaddamar da aka shafe ana yi kan tikitin takarar gwamnan PDP, bayan an ƙalubalanci zaɓen fidda gwani na farko da ya shafi Pantami, kafin daga bisani aka sake gudanar da zaɓen fidda gwani.
Hamma Saleh ya kuma bukaci magoya bayansa da su haɗa kai da APC domin tunkarar zaɓen da ke tafe.
