Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar ADC ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da hannu a hare-haren da ake kai wa jam’iyyun adawa yayin tarukan siyasa a Najeriya.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaranta, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, ADC ta bayyana matakin APC na yin Allah-wadai da hare-haren a matsayin ƙoƙarin kawar da hankalin jama’a daga zarge-zargen da ake yi mata.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa wasu magoya bayan APC na tarwatsa tarukan adawa, lalata allunan yaƙin neman zaɓe da kai hare-hare kan ‘ya’yan jam’iyyun adawa a wasu jihohi.
ADC ta kuma danganta tarwatsa wani taron jam’iyyar NDC da aka shirya gudanarwa a Legas ranar Alhamis da abin da ta kira dabarun tsoratar da ’yan adawa.
Ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa na gudanar da ayyukansu cikin zaman lafiya da ’yanci gabanin babban zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta ce tana tattara bayanan hare-haren da take zargin an kai wa mambobinta domin miƙa su ga hukumomin da suka dace.
Sai dai sanarwar ba ta gabatar da hujjojin da ke tabbatar da hannun APC a hare-haren ba, kuma ba a samu martanin jam’iyyar mai mulki kan waɗannan zarge-zarge a cikin sanarwar ba.
