Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta bayyana wani sabon tsari na kasa mai suna One Humanitarian, One Poverty Response System (OHOPRS) da nufin fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga talauci cikin shekaru biyar masu zuwa.
Ministan ayyukan jin kai da rage talauci, Bernard Doro, ya bayyana cewa an kirkiro shirin domin magance talauci ta fannoni da dama, ta hanyar amfani da bayanai na zamani, hadin kai da kuma tsarin da ke mayar da hankali ga jama’a.
A cewarsa a tsarin na shekarun 2026 zuwa 2030 da aka gabatar a Abuja, gwamnati na shirin tara Naira tiriliyan 16 domin aiwatar da shi.
Ya ce duk da yawan kudaden da ake kashewa wajen rage talauci, ba a samun sakamako mai gamsarwa, yana mai cewa sama da kashi 63 cikin 100 na yan Najeriya na fama da talauci mai fadi.
Ministan ya kuma ce manufar shugaban kasa, Bola Tinubu, ita ce fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga talauci kafin shekarar 2030 tare da tabbatar da gaskiya ta hanyar fasahar zamani.
A nasa bangaren, jami’in kula da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mohamed Fall, ya ce talauci a Najeriya ya zama matsalar gaggawa.
Ya ce kashi 62 cikin 100 na ‘yan Najeriya na rayuwa cikin talauci, yayin da mutane miliyan 33 ke fama da matsanancin rashin abinci, don haka akwai bukatar sabon tsari mai hade dukkan bangarori.
Shi ma shugaban Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), Adeyemi Adeniran, ya ce kimanin mutane miliyan 133 a Najeriya na fama da talauci mai yawa bisa rahoton shekarar 2022.
Ya jaddada cewa babu wata hukuma guda da za ta iya magance matsalar talauci ita kadai, don haka akwai bukatar hadin kai tsakanin gwamnati, kungiyoyin kasa da kasa, kungiyoyin farar hula da kuma bangarori masu zaman kansu.
An tsara cewa Gwamnatin Tarayya za ta bayar da Naira tiriliyan 1.5, abokan hulda za su bayar da Naira biliyan 800, bangarori masu zaman kansu da zuba jari za su bayar da Naira biliyan 600, yayin da kudaden bangaren kasa da kasa za su bayar da biliyan 300, wanda zai kai jimillar Naira tiriliyan 3.2 a kowacce shekara.
Haka kuma, gwamnati na shirin kaddamar da Asusun Kasa na Ayyukan Jin Kai da Rage Talauci, ta hanyar sabbin hanyoyin samar da kudi kamar su kudaden yanayi, na zamantakewa, zuba jari daga kamfanoni, da kuma tsarin kudin Musulunci kamar Zakka, Sukuk da Waqf.
Domin tabbatar da gaskiya da ingantaccen tsarin gudanarwa, an samar da hanyar sa ido mai karfi da ya hada da kwamitin kasa, bangaren bincike mai zaman kansa, tsarin biyan kudi bayan samun sakamako da kuma tsarin sa ido na zamani ta hanyar fasaha.
