Kungiyar Dalibai Ta Kasa reshen jihar Kano, ta yi kira da babbar murya ga manyan makarantun gaba da sikandire a jihar da su fito da wani salon hukunta dalibai a maimakon korarsu baki daya daga makarantar.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar Kwamared Muddassir Hamza Dankaka ne ya yi kira a madadin shugabannin kungiyar, yana mai cewa korar daliban baki daya daga makaranta na zama barazana ga tsaro da zaman lafiyar jihar Kano.
- Kungiyar ASUU ta janye yajin aikin gargadi da ta
- Kungiyar Tsoffin Daliban Jami’ar Bayero Kano Sun Gudanar da Taron Sada Zumunta Karo na 35
- NANS ta baiwa gwamnatin tarayya da ASUU wa’adin kwanaki don su warware rikicin da ke tsakaninsu
“Duba da yadda matsalar ke ci gaba da samun wajen zama a tsakanin jami’o’in ya sanya muka ga dacewar kirkiro wani kamfe don fadakar da mahukunta illar dake tattare da korar dalibai musamman bayan samunsu da laifin satar amsa yayin jarrabawa”. In ji shi.
A watan Satumbar shekarar nan jami’ar Bayero ta sanar da korar dalibai har guda 57 da ta kama da laifuka daban-daban da suke da alaqa da satar amsa yayin jarrabawa, matakin da kungiyar ta shirya daliban ta shirya ganin an samu sauyi a hukuncin.
