A yau Asabar ne ake bikin baje kolin kayayyaki karon na 45 a Kano.
Bikin wanda aka saba yi duk shekara Kungiyar Noma da Kasuwanci da kuma Masana’antu (KACCIMA) ta jihar ce ke shirya wa a babban filin bajen kolin da ke babban birnin jihar.
Za a kwashe makonni biyu a wannan baje kokin da manyan kamfanoni daga cikin da kuma wajen jihar ke halarta.
Bikin budewar na yau ya samu halartar manyan baki daga ciki da kuma wajen kasar nan ciki har Ministan Tsaro kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Badaru Muhammad.