Manyan ’yan siyasa a Najeriya ne sauka a Jihar Kano domin halartar ɗaurin auren ’yar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ɗan Dahiru Mangal.
A ranar Asabar ne aka a ɗaura auren Dokta Aisha Rabiu Musa Kwankwaso da angonta, Injiniya Fahad Dahiru Mangal a birnin na Dabo
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, na daga cikin manyan ’yan siyasar da yanzu haka sun sauka a Birnin na Dabo.
Daga cikin tsofaffin gwamnonin da suka halartarci bikin akwai Ahmed Makarfi na Jihar Kaduna da Abdulaziz Abubakar Yari na Jihar Zamfara da Isa Yuguda na Jihar Bauchi da Adamu Aliero na Jihar Kebbi.
Sauran tsofaffin gwamnonin sun haɗa da Lucky Igbinedion na Jihar Edo da Mahmud Shinkafi na Jihar Zamfara da Victor Attah na Jihar Akwa Ibom.
Irin wannan taro na ɗaurin auren ya zama tamkar wani taron sake ganawa da juna bayan shekaru tsakanin manyan ’yan siyasar Najeriya.