Saurari premier Radio
22.4 C
Kano
Monday, September 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin Jihar Kano Ta Sanar Da Kammala Tsaface Shirin Tallafawa Ilimin Yaya...

Gwamnatin Jihar Kano Ta Sanar Da Kammala Tsaface Shirin Tallafawa Ilimin Yaya Mata Na AGILE

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta kammala tsaface shirin bunkasa ilimin yaya mata na AGILE domin yin dai-dai da tarbiyya da al’adun jihar.

Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ce ta tsaftace shirin da hadin gyiwar masu ruwa da tsaki, inda aka gudanar taron kwanaki biyu tare da tabbatar da an cire duk wani bangare da ake ko kwanto a kansa da kuma kara wasu abubuwa da za su inganta ilimin yaya mata a jihar Kano.

Da yake jawabi bayan kammala taronw, kamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya ce ma’aikatar ta kara fito da sabbin tsare-tsare da za su kara inganta shirin na AGILE, wadanda za su yi dai-dai da tarbiyya da yanayin rayuwar al’ummar jihar Kano.

Kwamishinan ya kuma musanta zarge-zargen da ake wa shirin na bata tarbiyyar yaya mata, inda yace shirin yana matukar muhimmanci wajen inganta ilimi tare da tallafawa gwamnati wajen bayar da kayan koyo da koyarwa ga dalibai.

A nasa bangaren, shugaban shirin a jihar Kano, Alhaji Nasiru Abdullahi-Kwalli, ya ce za a fassara abubuwan da shirin ya kunsa da wanda aka gudanar a yayin taron karawa juna sanin zuwa harshen Hausa da Larabci domin al’umma su fuskanta.

Ya kara da cewa makasudin wannan taro da suka shirya, shi ne wayar da kan masu ruwa da tsaki dangane da abunda shirin ya kunsa tare da lalubo hanyoyin inganta shi.
Shekh Nasir Adam, wanda shi ne shugaban limaman masallatan Juma’a na jihar Kano, ya ce sun gamsu da tsarin da gwamnatin Kano da ma’aikatar ilimi suka yi, saboda haka al’umma su daina kyamar shirin.

AGILE wani shiri ne da ke samun tallafi daga bankin duniya, wanda ke tallafawa ilimin yaya mata masu tasowa daga shekaru 10 zuwa 20, inda ake tallafa musu ta bangaren ilimi da sana’o’i.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...