Saurari premier Radio
22.3 C
Kano
Tuesday, September 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciDilolin siminti sunyi martani game da rage farashin da kamfanin BUA yayi

Dilolin siminti sunyi martani game da rage farashin da kamfanin BUA yayi

Date:

Manyan dilolin siminti a kasar nan sun fara maida martani kan sanarwar kamfanin BUA na rage farashin simintin zuwa naira 3500 a makon nan.

A tattaunawarsu da Premier Radio, wasu daga cikin manyan dilolin Simintin a nan Kano da Jihar Katsina sun ce har yanzu al’umma basu fahimci abinda ragin ke nufi ba, suka ce 3500 da kamfanin ya bayyana, farashin kamfani ne kawai, amma bayan nan akwai kudin dako mai dan karan tsada da suke biya domin kai simintin jihohin su, wanda hakan kan sa farashin ya tashi.

Haka zalika yan kasuwar sun bada shawarar cewa in har kamfanin da gaske yake yi, to ya tabbatar simintin ya kai ga dilolin har jihohin su a wannan farashi na 3500, wato dai motocin kamfanin su dinga kai simintin kyauta, hakan ne kadai zai sanya talaka yaga saukin a fili.

Kafin yanzu dai kamfanin na BUA na ta shan addua da samun yabo daga alummar kasar nan. Kan wanna naimijin kokari da aake gani yayi a wannan lokaci da jamaa ke fama da matsin tatatali arziki.

Koda muka tuntubi guda cikin shugabanin kamfanin na Bua ya ce bashi da hurumin yin magana a yanzu sai dai nan gaba idan ya samu izinin yin magana.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...