Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da motocin kula da marasa lafiya samfurin tafi da gidanka masu ƙafa 3, waɗanda suke ɗauke da kayan bayar da agajin gaggawa ga masu jinya ga dukkan mazabu 484 da ke ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Shirin mai suna Abba Gida-Gida Rural Ambulance Service, an ƙirƙire shi ne domin sauƙaƙa jigilar marasa lafiya zuwa asibitoci cikin gaggawa, musamman a yankunan karkara da ke fama da matsalar hanyoyi da nisan wuraren kiwon lafiya.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin, Gwamna Abba ya ce an bullo da tsarin ne domin magance ƙalubalen da mata masu juna biyu, yara, waɗanda suka samu haɗarin mota da sauran marasa lafiya ke fuskanta wajen samun kulawar gaggawa ko jigilar su akan lokaci zuwa asibiti.
Gwamnan ya jaddada cewa ingantaccen tsarin kiwon lafiya bai tsaya ga gina asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko kawai ba, har da samar da hanyoyin kai marasa lafiya asibiti cikin lokaci.
Shi ma a nasa jawabin, Sarkin Kano Muhammad Sanusi na II ya gargadi direbobin motocin da ma’aikatan da zasu yi aiki da zasu kula da marasa lafiyar, da su ji tsoon Allah wajen gudanar da ayyukansu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na buƙatar sarakunan gargajiya, malaman addini, shugabannin al’umma, kansiloli da ma’aikatan lafiya da su ba shirin goyon baya tare da kula da motocin, tare da umartar shugabannin ƙananan hukumomi da waɗanda aka damƙawa motocin da su tabbatar da kula da su, amfani da ƙwararrun ma’aikata wajen gudanar da aikin da kuma hana amfani da su wajen wasu abubuwan da ba su dace da manufar shirin ba.
